Bale ya gargadi Real Madrid kan lafiyarsa
Gareth Bale na Wales ya bukaci Real Madrid kar ta kuskura ta wallafa bayanan lafiyarsa, saboda yana da damar kin amincewa da wallafa bayanan kamar yadda dokar Spain ta zayyana.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jaridar Marca ta ce, Kungiyar Kwallon Kafa ta Shanghai Shenhua ta sake yunkurawa domin sayen Bale daga Real Madrid.
Ko a ranar Litinin, sai da dan wasan ya yi balaguro zuwa birnin Laondon domin ganawa da dillalinsa a daidai lokacin da ake ganin makomarsa ba ta da tabbas a Real Madrid.
Kodayake Real Madrid ta ce, Bale ya ziyarci London ne saboda wasu dalilai na kashin kansa.
Kiris ya rage dan wasan ya koma China a kakar da ta gabata domin ci gaba da taka leda amma Real Madrid ta haddasa tarnakin da ya hana shi raba gari daita a wancan lokacin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu