Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Mbappe na PSG zai shafe makwanni 4 ya na jinyar rauni

Kungiyar kwallon kafa ta PSG da ke Faransa, ta tabbatar da cewa dan wasanta Kylian Mbappe zai yi jinyar makwanni bayan raunin da ya samu a cinya yayin karawarsu da Toulouse shekaran jiya Lahadi karkashin gasar Lig 1.

Dan wasan PSG Kylian Mbappe bayan samun rauni a wasansu da Toulous
Dan wasan PSG Kylian Mbappe bayan samun rauni a wasansu da Toulous REUTERS/Charles Platiau
Talla

Baya ga Mbappe, shima Edinson Cavani zai yi jinyar makwanni 3 kan rauninsa da shima ya samu qugu yayin wasan ko da dai shi zai samu damar taka leda a wasan farko na rukuni karkashin gasar cin kofin zakarun Turai ranar 17 ko kuma 18 ga watan Satumba.

Matashin dan wasan na PSG wanda ke rike da kofin duniya, a tsawon makwannin da zai dauka ya na jinya zai rasa wasannin Lig har guda 3 yayinda zai rasa damar takawa kasarsa leda a wasannin neman gurbin shiga gasar Euro 2020 da Faransa za ta karbi bakonci Albania da Andorra cikin wata mai kamawa.

Alamu dai na nuni dacewa PSG ka iya fuskantar matsala la’akari da yadda raunin ‘yan wasan biyu ke matsayin kari kan rashin tabbas din makomar Neymar a Club din, kuma ko da ace Neymar ya na nan to fa dan wasan na fuskantar dakatarwa daga wasanni ukun farko na gasar cin kofin zakarun Turai bayan rashin da’ar da ya nuna kan alakalan wasa a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.