Isa ga babban shafi
Wasanni

"Cin zarafin 'yan wasa zai haifar da abinda ya faru a 1995"

Tsohon dan wasan Tottenham, Gareth Crooks ya yi kashedin cewa, za a iya sake samun makamancin yanayin da ya tilasta Eric Cantona kai wa wani magoyin bayan Crystal Palace duka da kafa a shekarar 1995, muddin gwamnati ta gaza daukar mataki kan matsalar cin zarafin ‘yan wasa.

Rashfor da Pogba
Rashfor da Pogba Reuters
Talla

Idan za a iya tunawa a shekarar 1995 ne, Cantona, tsohon dan wasan Manchester United ya yi tsalle irin na salon fadan Kung-Fu, inda ya doki wani mai goyon bayan Crystal Palace bayan ya zarge shi da cin zarafinsa a yayin wasan da Manchseter United ta buga a Selhurt Park a watan Janairun shekarar ta 1995.

Kashedin da Crooks ya yi na zuwa ne bayan an ci zarafin ‘yan wasan Manchester United wato Paul Pogba da Marcus Rashford a shafukan sada zumunta bayan sun barar da bugun fanariti.

Pogba ne ya fara barar da bugun fanaritin a wasansu da Wolves, sannan shi ma Rashford ya barar a wasansu da Crystal Palace a ranar Asabar da ta gabata, abinda ya sa magoya baya ke caccakar su a shafukan sada zumunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.