Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Man United na da kwarin gwiwar ci gaba da rike De Gea- Solskjaer

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce ya na da kwarin gwiwar cewa mai tsaron ragar Club din David De Gea zai amince da tsawaita kwantiraginsa don tunkarar sabuwar kakar wasa mai zuwa.

David De Gea mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United
David De Gea mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Reuters / Lee Smith Livepic
Talla

United dai na tunkarar wasannin sharen fagen shiga sabuwar kakar wasa ne cike da zullumin rabuwa da De Gea wanda kwantiraginsa ke karewa kuma ake rade-radin yiwuwar komawarsa PSG ta Faransa.

United dai ta yiwa De Gea tayin biyansa yuro dubu 350 a matsayin albashin kowanne mako banda alawus-alawus matakin da zai mayar da shi mai tsaron raga mafi daukar albashi a tarihin kwallo.

Ana dai sanya De Gea a matsayin mai tsaron raga mafi hazaka a duniyar kwallo, duk da cewa dai Club din say a gaza kai labari a gasar Firimiya da ma ta zakarun Turai.

Cikin jawabin Solskjaer ga manema labarai ya ce mai tsaron ragar ba zai halarci wasansu na ranar Asabar da za su kara da Perth Glory ba amma akwai tabbacin zai kasance a sauran wasanninsu yayin ziyarar kwanaki 10 da za su yi a Australia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.