Isa ga babban shafi
Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Ban fidda ran kai wa wasan karshe ba -Pochettino

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino ya ce har yanzu suna da sauran damar zuwa wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai bayan rashin nasara har gida a hannun Ajax da kwallo daya mai ban haushi.

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino Reuters/Hannah McKay Livepic
Talla

A cewar Pochettino yayin wasansu na larabar makon gobe za su iyakar kokarinsu wajen ganin sun rama kwallonsu tare da ratatawa Ajax wasu tarin kwallaye don zarcewa wasan karshe wanda za su kara da ko dai Liverpool ko kuma Barcelona.

Dama dai akwai hasashen Ajax ka iya kai labari a wasan na jiya ganin yadda Tottenham ta doka wasan ba tare da wasu zakakuran ‘yan wasanta ba, wadanda suka hada da Harry Kane, da Erik Lamela da Harry Winks wadanda ke jinyar rauni, sai kuma Son Heung-min da ke fuskantar dakatarwa daga doka wasa guda bayan abin da ya faru a wasansu da Manchester City watan jiya karkashin gasar.

Haka zalika Za a iya cewa dai akwai aiki babba a gaban Tottenham, wadda ke fatan dage kofin karon farko a tarihi, domin kuwa kungiyar ta Ajax yanzu ta fara zama ba kanwar lasa ba, la’akari da yadda ta yi waje da Real Madrid a zagayen kungiyoyi 16 kana ta fitar da Juventus a zagayen kungiyoyi 8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.