Isa ga babban shafi
wasanni

Herrera zai koma PSG saboda Man-U ta ki biyan sa

Dan wasan Manchester United Ander Herrara mai shekaru 29 ya cimma wata kwarya-kwaryar matsaya da PSG domin ci gaba da taka leda tare da ita bayan Manchester United ta ki amincewa da muradinsa na karin albashi.

Ander Herrera
Ander Herrera skysports.com
Talla

Jaridar Daily Record ta ce, dan wasan ya dauki wannan makin ne na komawa PSG bayan rashin gamsuwa da albashin da Manchester United za ta ci gaba da ba shi a karkashin sabuwar doguwar yarjejniyarsa da ita.

Manchester United na biyan dan wasan Pam dubu 80 a mako guda, amma yanzu yana bukatar ta rika biyan sa Pam dubu 200 a duk mako.

Sai dai Manchester United din ta ki sauya matsayarta game da karin albashin nasa, duk da cewa, yana cikin zaratan ‘yan wasan da kocinsu, Ole Gunnar Solskjaer ke ji da su.

Solskjaer ya ce, Herrera dan wasa ne mai kuzari da juriya, abinda ya sa yake matukar burin ci gaba da aiki da shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.