Isa ga babban shafi
Wasanni

Pogba ya soma kokarin sauya sheka zuwa Real Madrid

Ga dukkanin alamu, komar kungiyar Real Madrid na shirin yin babban kamu a fegen wasanni, bayan da jaridar Marca da ke kasar Spain ta rawaito cewa ya tabbata dan wasan Manchester United Paul Pogba ya soma yunkurin sauya sheka zuwa kungiyar ta Real Madrid a karshen kakar wasa ta bana.

Paul Pogba.
Paul Pogba. Reuters/Jason Cairnduff
Talla

A zamanin da Jose Mourinho ke horar da Manchester United dai Pogba yayi yunkuri ne na komawa tsohuwar kungiyarsa ta Juventus, sakamakon sabanin da ya rika samu da Mourinho, sai dai daga bisani dan wasan ya janye aniyar tasa, bayan da ole Gunnar Solskjaer yam aye gurbin Mourinho.

Duk da sauyin daya samu, Jaridar Marca ta rawaito cewa Pogba ta hannun wakilinsa Mino Raiola ya dukufa wajen ganin tabbatar komawarsa Spain a karshen wannan kaka.

Zalika rahoton ya ce kocin Real Madrid Zinaden Zidane da a yanzu kungiyar ta amincewa masa kasha euro miliyan 300 wajen sayen ‘yan wasa, a shirye yake ya kulla yarjejeniya da Pogba, la’akari da cewa dan wasan na daga cikin wadanda Zidane ke kokarin ya sauya zubin Real Madrid da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.