Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta musanta soma tuntubar Pogba

Daraktan wasanni na Barcelona kuma tsohon dan wasanta mai tsaron baya, Eric Abidal, ya musanta rahotannin da ke cewa, ya gudanar da wani taron sirri tsakaninsa da Paul Pogba kan yiwuwar sauyin sheka daga Manchester United zuwa kungiyar.

Paul Pogba na kungiyar Manchester United, yayin murnar lashe gasar cin kofin duniya ta 2018, da tawagar 'yan wasansu na kasar Faransa suka yi a Rasha.
Paul Pogba na kungiyar Manchester United, yayin murnar lashe gasar cin kofin duniya ta 2018, da tawagar 'yan wasansu na kasar Faransa suka yi a Rasha. REUTERS/Carl Recine
Talla

Rahotanni daga wasu kafofin yada labaran turai sun rawaito cewa Abidal ya gana da Pogba ne a birnin Los Angeles, sai dai daraktan ya musanta hakan, inda ya ce harkokinsa ne kawai suka kais hi Amurka, kuma bai yi yunkurin tuntubar Pogba ba duk da yana labarin shima yana garin.

Abidal ya tabbatarwa Manchester United cewa ba zai soma tuntubar kowane dan wasanta da nufin jan sa zuwa Barcelona ba har sai ya sanar da kungiyar.

A shekarar 2016, United ta sayo Pogba kan kudi mafi tsada a lokacin na fam miliyan 89 daga Juventus, sai dai jim kadan bayan sauyin shekar, dan wasan ya fara cin karo da matsaloli, tsakaninsa da mai horarwa Jose Mourinho.

Zargin samun rashin kyawun alaka tsakanin Pogba da Mourinho ya karfafa ne a kakar wasan da ta gabata, inda kocin na Manchester United ya rika ajiye dan wasan mafi tsada a kungiyar a benci, a wasu muhimman wasannin da ya kamata a ce ya buga mintuna 90 a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.