Isa ga babban shafi
Wasanni

An kammala gasar Olympics ta nakasassu

An kawo karshen gasar Olympics ta masu fama da larurar nakasa ta duniya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta karbi bakunci.

Akalla yan wasan dubu 7 ne daga kasashen duniya suka shiga gasar Olympics ta mas fama da larurar nakasa ta 2019 da Hadaddyar Daular Larabawa ta karbi bakunci.
Akalla yan wasan dubu 7 ne daga kasashen duniya suka shiga gasar Olympics ta mas fama da larurar nakasa ta 2019 da Hadaddyar Daular Larabawa ta karbi bakunci. Reuters/Mike Blake
Talla

A ranar 14 ga watan Maris da muke ciki aka soma gasar wasannin motsa jikin ta masu fama da larurar nakasa ta duniya a birnin Abu Dhabi inda kasashe daban daban suka fafata a wasanni 24.

Kasashen da ke kan gaba wajen lashe adadin lambobin yabo mafi yawa a gasar ta Olympics, sun hada da mai masaukin baki Hadaddiyar Daular Larabawa da kasar India.

India ta lashe Zinare 60, Azurfa 83 da kuma Tagulla 90, yayinda mai masaukin baki, Hadaddiyar Daular Larabawa da ta samu Zinare 47, Azurfa 43 da kuma Tagulla 54.

Yan wasa 60 da suka wakilci Najeriya a gasar Olympics din ta masu fama da larurar nakasa, sun taka rawar gani wajen samun lambonin yabo na Zinare, Azurfa da kuma tagulla, bayan fafatawa a wasanni guda 8, da suka hada da kwallon kafa, kwallon tebur, linkaya, kwallon Kwando da kuma tseren Keke sai Badminton.

Tawagar ‘yan wasan motsa jikin na Najeriya sun samu lambobin yabon da suka hada da Zinare 9, Azurfa 7 da kuma Tagulla 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.