Genoa ta dakile yunkurin Juventus na kafa tarihi a Seria A
Genoa ta lallasa Juventus da kwallaye 2-0 a gasar Seria A ta kasar Italiya, abinda kawo karshen jerin wasannin da Juventus ke bugawa ba tare da shan kaye ba a gasar.
Wallafawa ranar:
Yayin wasan na jiya, kocin Juventus Massmilano Allegri, ya hutar da dan wasansa Cristiano Ronaldo, wanda ya ciwa kungiyar dukkanin kwallaye uku da ta lallasa Atletico Madrid a gasar Zakarun Nahiyar Turai, matakin da wasu magoya bayan Juventus ke ganin ya taka rawa wajen kayen da suka sha a hannun Genoa.
Dan wasan Genoa Stefano Sturaro ne ya jefa kwallon farko ragar Juventus a mintuna na 72, yayinda Goran Pandev ya kara kwallo ta biyu yayinda ya rage mintuna 9 a tashi daga wasa.
Juventus ke jagorantar gasar ta Seria A da maki 75, Napoli a matsayi na 2 da maki 60, sai ta uku Inter Milan da maki 53, yayinda AC Milan ke matsayi na 4 da maki 51.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu