Isa ga babban shafi
Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Ronaldo ya dara Messi zura kwallo a gasar zakarun Turai

Bayan nasarar ratata kwallaye har 3 shi kadai a ragar Atletico Madrid jiya Talata, yanzu kenan Cristiano Ronaldo na Portugal na da jimullar kwallaye 124 a wasannin gasar inda ya dara takwaransa na Barcelona dan Argentina Messi da kwallaye 18.

Cristiano Ronaldo na Juventus kenan lokacin da ya ke zura kwallonsa na biyu minti 4 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci
Cristiano Ronaldo na Juventus kenan lokacin da ya ke zura kwallonsa na biyu minti 4 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Massimo Pinca/Reuters
Talla

Haka zalika yanzu haka Cristiano Ronaldo ya wuce gaban Messi a nasarar zura kwallaye 3 a wasa daya, wanda aka fi sani da hat-tricks a turance, inda ya yi makamanciyar nasarar har sau 8 a gasa daban-daban.

Bayan nasarar ta Juventus kan Atletico a wasan na jiya, wannan ya nuna cewa, cikin shekaru 4 da suka gabata, ba a iya cire duk wani Club da Ronaldo ke cikinsa a gasar ta zakarun Turai.

Yayinda idan har Ronaldo mai shekaru 34 ya yi nasarar dage kofin na zakarun Turai a wannan karon kai tsaye ya kamo Francisco Gento dan wasan Real Madrid da ya kafa tarihin lashe kofin har sau 6 a tarihinsa na Kwallo.

A bara ne dai Juventus ta amince da sayen Cristiano Ronaldo daga Real Madrid kan kudi fiye da yuro miliyan 99, a wani mataki na ganin Club din ya yi nasarar dage kofin a wannan karon, wanda rabonsa da shi tun a shekarar 1996.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.