Isa ga babban shafi
Wasanni

Har yanzu mun kasa cike gurbin Ronaldo a Madrid - Modric

Dan wasan Real Madrid kuma mai rike da kyautar gwarzon tamaula a duniya, Luka Modric, ya ce har yanzu, ‘yan wasan gaba na kungiyar sun kasa cike gibin da Cristiano Ronaldo ya bari.

'Yan wasan Real Madrid Luka Modric da Gareth Bale, tare da tsohon dan wasan kungiyar Cristiano Ronaldo.
'Yan wasan Real Madrid Luka Modric da Gareth Bale, tare da tsohon dan wasan kungiyar Cristiano Ronaldo. REUTERS/Sergio Perez
Talla

Modric ya bayyana koken ne, yayin da suke shirin tunkarar fafatawarsu da Ajax yau Talata, a gasar zakarun turai, inda za su karbi bakuncin kungiyar a Santiago Bernabeau. A zagayen farko na fafatawar dai Real Madrid ce ta yi nasara da kwallaye 2-1 akan Ajax.

Gwarzon dan wasan ya ce tun bayan rabuwa da Cristiano Ronaldo da ya koma Juventus, Real Madrid ta gaza ci gaba da nuna kwazo a fage yawan zura kwallaye da kuma samun nasarori kamar yadda lamarin yake a baya.

Bayan rabuwa da Ronaldo, Real Madrid ta sayi ‘yan wasa masu kananan shekaru da suka hada da Vinicius Junior da mariano Diaz, sai dai babu wani shahararren dan wasa da ta sayo domin maye gurbin da Ronaldo ya bari.

A tsawon kusan shekaru 10 da Ronaldo ya shafe tare da Real Madrid, ya ci mata kwallaye 451, a wasanni 438 da ya buga mata. Sai dai bayan tafiyarsa Juvenus da kuma ajiye aiki da tsohon kocinsu Zinaden Zidane yayi, kungiyar ta soma fuskantar matsaloli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.