Isa ga babban shafi
wasanni

Aikina na cikin barazana a Chelsea- Sarri

Kocin Chelsea, Maurizio Sarri ya ce, aikinsa na horarwa na fuskantar barazana bayan lallasar da suka sha a hannun Manchester City da ci 6-0 a gasar firimiyar Ingila.

Kocin Chelsea, Maurizio Sarri
Kocin Chelsea, Maurizio Sarri reuters
Talla

A karon farko kenan tun shekarar 1991 da Chelsea ke shan mummunan kashi irin wannan a hannun wata kungiya a gasar firmiyar Ingila, in da a wancan lokaci, Nottingham Forest ta yi ma ta dukan- kawo-wuka da ci 7-0.

Sarri da kaften din Chelsea, Cesar Azpilicueta sun bai wa magoya bayan kungiyar hakuri kan lallasar da suka sha a hannun Manchester City a Etihad, abin da ya rikito da  kungiyar zuwa mataki na 6 a teburin gasar.

Sargio Aguero ya sake taka muhimmiyar rawa a fafawar ta ranar Lahadi, in da ya jefa kwallaye uku shi kadai, yayin da Manchester City ta sake komawa saman teburin gasar da maki 65, in da sake karbe ragama daga hannun Liverpool.

Ita ma Tottenham ta yi nasara akan Leicester City da ci 3-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.