Isa ga babban shafi
wasanni

Solskjaer ya kafa tarihi a Manchester United

Kocin rikon kwarya na Manchster United, Ole Gunnar Solskjaer ya kafa tarihin zama mutun na biyu da ya samu nasara a wasanni hudu da ya fara jagoranta a jere, in da a baya-bayan nan ya samu nasara akan Newcastle da ci 2-0 a gasar firimiyar Ingila.

Ole Gunnar Solskjaer, kocin rikon kwarya a Manchester United
Ole Gunnar Solskjaer, kocin rikon kwarya a Manchester United Svein Ove Ekornesvaag / NTB SCANPIX / AFP
Talla

Yanzu haka Solskjaer ya bi sahun Sir Matt Busby, kocin da ya fara kafa tarihin samun nasara a wasannin hudu da ya fara jagoranta a shekara 1956 a Manchester United.

Romelu Lukaku da Marcus Rashford ne suka ci wa Manchester United kwallayen biyu a fafatawarsu da Newcastle a ranar Laraba.

Kocin  ya karbi aikin horar da Manchester United ne bayan ta sallami Jose Mourinho da ya gaza kai kungiyar ga gaci a wannan kaka.

A bangare guda, Solskjaer ya ce, ba ya fatan barin Manchester United a cikin wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.