Isa ga babban shafi
Wasanni

Modric ya soki Messi da Ronaldo kan kauracewa bikin Ballon d'Or

Sabon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Luka Modric ya soki, Cristiano Ronaldo da Lionel Messi dangane da kauracewa halartar bikin mika masa kayutar Ballon d’Or da ya lashe ta bana.

Luka Modric na kungiyar Real Madrid.
Luka Modric na kungiyar Real Madrid. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Modric ya ce kin halartar taron da tsaffin gwarazan kwallon kafar suka yi, rashin adalci ne ga sauran takwarorinsu ‘yan wasa, masoya kwallon kafa, da kuma wadanda suka kada kuri’unsu wajen zaben gwarzon dan wasan na bana.

A cewar Modric matakin na Ronaldo da Messi ya nuna cewa, kyautukan karrama gwarzon dan kwallon kafa na duniya basu da muhimmanci, idan ba su aka mikawa ba.

A watan da ya gabata Modric ya kawo karshen shekaru goma da Messi da Ronaldo suka shafe suna lashe kyautukan FIFA da Ballon d’Or na gwarzayen kwallon kafa na duniya.

Modric ya taka rawa wajen taimakawa kungiyarsa ta Real Madrid ta lashe kofin gasar zakarun turai karo na uku a jere, sai kuma taimakawa kasarsa Croatia wajen kaiwa matakin wasan karshe na farko a tarihi, na gasar cin kofin duniya da Rasha ta karbi bakunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.