Rooney zai jagoranci Ingila a wasansa na karshe
Wayne Rooney da ya fi kowanne dan wasan Ingila zura kwallaye a tarihi zai kasance kaften din tawagar kasar a wasan da za su yi da Amurka a ranar Alhamis, wasan da zai kasance na bankwana ga Rooney.
Wallafawa ranar:
Rooney mai shekaru 33 ya yi ritaya daga buga wa Ingila tamaula a shekarar 2017, amma duk da haka zai buga wasansa na karshe kuma na 120 a fafatawar ta yau.
An dai shirya cewa, Fabian Delp zai fara daura igiyar kaften din tawagar ta Ingila kafin daga bisani ya mika ta ga Rooney a zagaye na biyu na wasan sada zumuntar.
Ronney ya jefa kwallaye 53 a wasannin da ya buga wa Ingila, yayin da kuma za a yi masa karramawa ta musamman a yau don tuna irin gudunmawar da ya bayar a fannin kwallon kafar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu