Isa ga babban shafi
Turai

Arsene Wenger ya bayyana dawowar sa a 2019

Tsohon mai horar da kulob na Arsenal a Ingila Arsene Wenger ya na sa ran dawowar  fagen kwallon kafa a matsayin mai horar da yan  wasa a shekara ta 2019. 

Arsenal Wenger tsohon mai horar da Kulob na Arsenal
Arsenal Wenger tsohon mai horar da Kulob na Arsenal Reuters/Scott Heppell
Talla

A karshen kakar da ta gabata ne Wenger mai shekaru 69 bayan share shekaru 22 a matsayin mai horar da Arsenal ya kawo karshen zamansa da kungiyar.

Sai dai tsohon kocin ya ce, akwai yiwuwar ya koma horar da tawagar wata kasa ko kuma ya koma Japan, in da ya taba horar da Nagoya Grampus Eight.

Wenger ya shaida wa jaridar Sky sports cewa, yanzu ya huta sosai, kuma a shirye yake ya koma bakin aikin bayar da horo, amma bai bayyana takamammen in da zai koma ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.