Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya na shirin halartar gasar kwallon kafar nakasassu ta duniya

Mai horar kungiyar kwallon kafa ta masu fama da nakasa na Najeriya Victor Nwenwe, ya bayyana kwarin gwiwar tawagarsa ta ‘Special Eagles’ za ta nuna bajinta a gasar da zata halarta a kasar Mexico.

Wasu daga cikin 'yan wasan kwallon kafar Najeriya masu fama da nakasa, da ake kira 'Special Eagles'.
Wasu daga cikin 'yan wasan kwallon kafar Najeriya masu fama da nakasa, da ake kira 'Special Eagles'. The Eagle Online
Talla

Nwenwe wanda ya bayyana alwashin yayin ganawarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya, ya ce yanzu haka ‘yan wasan na Najeriya wato Special Eagles sun dukufa wajen atasye a Legas domin tunkarar wannan gasa.

A ranar 24 ga watan Oktoba da muke ciki, za'a soma gasar cin kofin duniya na kwallon kafar masu fama da nakasa, wadda zata kare a ranar 5 ga watan Nuwamba.

Najeriya dai na rukuni na 5, tare da Rasha, Brazil da kuma El Salvador.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.