Isa ga babban shafi
Wasanni

'Yan wasan kungiyoyin Spain sun janye aniyar shiga yajin aiki

Kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa da ke bugawa kungiyoyin kasar Spain wasanni a gasar La liga, sun janye aniyarsu ta shiga yajin aiki, dangane da adawar da suke da sabon shirin fafata wasu wasannin gasar ta La liga a Amurka.

Shugaban kungiyar 'yan wasan da ke bugawa fafata wasanni a kungiyoyin kwallon kafar kasar Spain a gasar La liga,  David Aganzo (Daga tsakiya),  yayin ganawa da manema labarai a birnin Madrid
Shugaban kungiyar 'yan wasan da ke bugawa fafata wasanni a kungiyoyin kwallon kafar kasar Spain a gasar La liga, David Aganzo (Daga tsakiya), yayin ganawa da manema labarai a birnin Madrid EFE-EPA/Kiko Huesca
Talla

Kungiyar ta yanke shawarar janye yajin aikin ne a jiya Laraba, bayan taron da ta gudanar, wanda ya samu halartar wasu daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyoyin da ke buga gasar La liga musamman kaftin kaftin da mataimakansu.

A makon da ya gabata ne, hukumar da ke shirya gasar La liga ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai tsawon shekaru 15, da wani kamfanin kafafen yada labarai da ke Amurka, wadda a karkashin yarjejeniyar za a rika buga wasu daga cikin wasannin La liga a Amurkan da nufin bunkasa wasan kwallon kafa a kasar.

Sai dai yarjejeniyar ba ta samu karbuwa ga kungiyar ‘yan wasan kungiyoyin kwallon kafar Spain, wadanda suka ce buga wasannin La liga a wajen kasar, zai nisanta su da dama daga cikin magoya baya, da sauran masu sha’awar kallon wasanninsu da ke kasar ta Spain.

Wani lokaci nan gaba ne za’a tattauna tsakanin kungiyar ‘yan wasan da kuma hukumar shirya gasar ta La liga domin warware wannan matsala.

Daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyoyin Spain da suka samu halartar taron na ranar Laraba, akwai, Sergio Ramos da Nacho dukkansu na Real Madrid, sai kuma Busquets da Sergio Roberto dukkansu daga Barcelona.

Sauran ‘yan wasan sun hada da, Leo Baptistao daga kungiyar Espanyol, sai kuma ‘yan wasan kungiyar Atletico Madrid Koke da Juanfran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.