Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool ta kai karar Salah wajen 'yan sanda

Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool ta shigar da karar dan wasanta Mohamed Salah ga jami’an ‘yan sanda bayan wani hoton bidiyo ya nuna shi karara yana latsa wayar salula alhalin yana cikin tukin mota.

Mohamed Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool ta Ingila.
Mohamed Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool ta Ingila. REUTERS/Phil Noble
Talla

Rundunar ‘yan sandan Merseyside ta tabbatar da mika bidiyon ga wani sashenta don gudanar da bincike.

An yi ta yada bidiyon a shafukan sada zumunta da ke nuna Salah wanda ya ci wa Liverpool kwallaye 44 a kakar da ta gabata, na latsa wayar a cikin motarsa wadda magoya bayansa da kananan yara suka kewaye ta.

Liverpool ta ce, za ta dauki nata matakin kan batun a cikin gida, amma ta ce, kawo yanzu, babu wani karin bayani da za a sake ji daga bakinta ko kuma daga bakin dan wasan na Masar.

Koda yake babu cikakken bayani kan ranar da aka dauki hoton bidiyon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.