Isa ga babban shafi
wasanni

Mbappe zai yi sadaka da dukkanin kudinsa

Dan wasan Faransa, Kylian Mbappe da tauraruwarsa ke haskawa a duniyar tamaula zai yi sadaka da dukkanin kudaden da ya samu a gasar cin kofin duniya ta bana da aka kammala a Rasha da yawanssu ya kai kimanin Naira miliyan 160.

Kylian Mbappé ya taimaka wa Faransa lashe kofin duniya a Rasha
Kylian Mbappé ya taimaka wa Faransa lashe kofin duniya a Rasha REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Rahotanni na cewa, dan wasan mai shekaru 19 da haihuwa zai taimaka wa marasa lafiya da ke kwance a asibiti da kuma kananan yara nakasassu da ke karkashin kulawar kungiya agaji ta Premiers de Cordee wadda ke horar da kananan yara da nakasassu kwallon kafa kyauta.

Dan wasan wanda ya fara taimaka wa kungiyar tun a bara, na ganin yin amfani da kudin wajen agaza wa al’ummar da ke cikin wani hali, shi ne mafi dacewa.

Mbappe ya samu kimanin Euro dubu 17 a dukkanin wasa guda da ya buga wa Faransa a Rasha, sannan ga karin Euro dubu 265 da ya samu daga nasarar lashe wa kasar kofin duniyar.

Dan wasan ya buga wasanni 7 a gasar, abin da ke nufin cewa a jumulce yana da Euro dubu 384, kwatankwacin Naira miliyan 153 da dubu 600 da ya samu a wannan gasa da aka kammala a karshen mako da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.