Isa ga babban shafi
Wasanni

"Wasan Faransa da Belgium na hamayya ne"

Nan da 'yan sa'o'i kalilan ne kasashen Faransa da Belgium za su kece raini a matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha, wasan da masharhanta ke cewa na hamayya ne, in da Faransa za ta yi amfani da kwazon Kylian Mbappe da Antoine Griezmann don ganin ta sama nasara akan Belgium wadda ke tinkaho da ‘yan wasa kamar Eden Hazard da Romelu Lukaku.

Kasashen Faransa da Belgium za su fafata da juna a wasan hamayya a gasar cin kofin duniya a Rasha
Kasashen Faransa da Belgium za su fafata da juna a wasan hamayya a gasar cin kofin duniya a Rasha golisports.com
Talla

Faransa na burin kaiwa matakin wasan karshe saboda raban da ta kai wannan mataki tun shekarar 2006, lokacin su Zinedine Zidane a Jamus.

Ita kuwa Belgium za ta jajirce ne a wasan don ganin ta kafa tarihin kaiwa matakin wasan karshe a karon farko a gasar cin kofin duniya.

Tarihi ya nuna cewa, Faransa ta doke Belgium a manyan wasanni uku da suka buga a can baya, da suka hada da wasanni biyu a gasar cin kofin duniya.

A bangare guda, a ranar Laraaba ne su ma kasashen Ingila da Croatia za su fafata da juna a matakin wasan dan da na karshe na gasar ta cin kofin duniyar.

Tuni masharhanta suka fara tsokaci kan wannan haduwa, in da manazarta kan kwallon kafa daga Birtaniya ke cewa, tilas ne Ingila ta takura dan wasan tsakiya na Croatia wato, Luka Modric matukar ta na son kaiwa wasan karshe a gasar.

Wani marubucin labarin wasanni a Birtaniya ya tunatar da jama’a irin barazanar da Modric ke da ita, in da ya ce, yana cikin tawagar da ta casa Ingila 2-0 a wani wasa da suka buga a shekarar 2006 a Zagreb a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin kasashen Turai.

Kazalika ana ganin kwarewar Modric wajen amfani da dukkanin kafafunsa biyu, ka iya zama karin barazana ga tawagar Ingila a wasan na ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.