Ban ji dadin yadda nahiyar Afrika ta gaza a Rasha ba - Infantino
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino, ya ce bai ji dadin yadda nahiyar Afrika ta gaza samun mai wakiltar ta ba, a zagayen gaba da na rukuni a gasar cin kofin duniya ta bana da ke gudana a Rasha.
Wallafawa ranar:
Kalaman na Infantino sun zo ne, bayan da dukkanin kasashe biyar, da suka hada da Najeriya, Morocco, Tunisia, Senegal da Masar, masu wakiltar nahiyar ta Afrika, suka fice tun a zagayen farko na gasar a matakin rukuni.
Karo na farko kenan da kasashen nahiyar Afrika suka gaza kai wa zagaye na gaba daga matakin rukuni a gasar cin kofin duniya, tun bayan irin haka da ya taba aukuwa a shekarar 1982.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu