Isa ga babban shafi
kwallon kafa

Masu horar da kwallo a Jamus sun karfafa gwiwar Loris Karius

Tawagar masu horar da ‘yan kwallo ta Jamus ta aike da sakon kara kwarin gwiwa ga mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Loris Karius bayan kura-kuran da ya tafka wanda ya kai Real Madrid ga lallasa Liverpool din da ci 3-1 a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai.

Loris Karius dai ya bar filin wasan a ranar asabar yana kuka kan abin da ya faru amma duk da haka wasu na ci gaba da yi masa barazana yayin wasu ke ganin ya kawo karshen wasan sa a Liverpool.
Loris Karius dai ya bar filin wasan a ranar asabar yana kuka kan abin da ya faru amma duk da haka wasu na ci gaba da yi masa barazana yayin wasu ke ganin ya kawo karshen wasan sa a Liverpool. REUTERS
Talla

Tawagar ta ce manufar aikewa da sakon shi ne ganin dan wasan bai karaya ba, sakamakon kura-kuran da ma sukar da yake ci gaba da fuskanta, wadda tawagar ta ce sukar ka iya haddasa masa matsala a gobensa.

A cewar Koepke wanda ya dage kofin duniya da kuma na zakarun Turai a 1990, bai kamata kura-kuran biyu su ja dogon zance har ma da barazana ga Karius dan Jamus mai shekaru 24 ba.

Tawagar kwaca-kwacan na Jamus ta kunshi shugabansu Joachim Loew da manajanta Oliver Bierhoff da kuma Koepke sun yi fatan kochiyan Liverpool Jurgen Klopp da manajojinta su karawa matashin mai tsaron ragar kwarin gwiwa don ganin bai karaya ba.

A martinin Koepke ga tsohon zakaran Jamus Lothar Matthaeus wanda ya bayyana kura-kuren na Karius da mafi muni da wani mai tsaron raga ya taba aikatawa cikin shekaru 30, ya ce Karius na daga cikin zakakuran masu tsaron raga da Jamus ta yi a Tarihi.

Loris Karius dai ya bar filin wasan a ranar asabar yana kuka kan abin da ya faru amma duk da haka wasu na ci gaba da yi masa barazana yayin wasu ke ganin ya kawo karshen wasan sa a Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.