Najeriya tana da zakakuran 'yan wasa - Simeone
Mai horar da kungiyar Atletico Madrid Diego Simeone, ya ce tawaga ta 2 ta ‘yan wasan Najeriya Super Eagles ta kunshi kwararru da zasu iya buga wasanni a manyan kungiyoyin kwallon kafa da ke nahiyar turai.
Wallafawa ranar:
Simeone ya bayyana haka ne bayan kammala wasan sada zumunci tsakanin ‘yan wasansa na Atletico Madrid da Najeriya inda suka samu nasara ta kwallaye 3-2, a filin wasa na Godswill Akpabio, da ke garin Uyo, na jihar Akwa Ibom.
Kocin na Atletico Madrid ya ce bayyana wasan da mai horarwa na Super Eagles Salisu Yusuf ya jagoranta da cewa ba wasa ne mai sauki ba, wanda ya kagu a kammala saboda fargabar yin rashin nasara a hannun ‘yan Najeriyar.
‘Yan wasan Najeriya Usman Mohammed da Kelechi Nwakali ne suka ci wa Super Eagles kwallayenta 2, yayinda Angel Correa, Fernando Torres da Borja Garces suka ci wa Atletico Madrid kwallaye 3.
A makon da ya gabata ne Atletico Madrid ta lashe kofin gasar Europa, bayan lallasa Marseille da kwallaye 3-0.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu