Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool ka iya nasara kan Madrid idan ta tsare gida- Lawrence

Tsohon mai tsaron gida na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Mark Lawrenson ya bukaci ‘yan wasan kungiyar su fi mayar da hankali wajen tsare gida maimakon yawaita kai hari don zura kwallo.

Tsohon dan wasan Liverpool Mark Lawrenson.
Tsohon dan wasan Liverpool Mark Lawrenson. Reuters
Talla

Lawrenson mai shekaru 60 wanda ya taka leda a Liverpool tsakankanin shekarun 1970 zuwa 1980 ya ce matukar Liverpool din ta yi makamancin wasan da ta yi a jiya tsakaninta da Roma yayin wasan karshe da za su kara da Real Madrid babu shakka baza su kai labarai ba.

A cewarsa Liverpool din ta kwaci kanta da kyar ne musamman bayan dawowa daga hutun rabin lokaci bayan da ta ga Romar na shirin shan ta musalla, inda ta sauya salon wasan daga kai hari zuwa kare kai, wanda dama a cewarsa tun farko salon wasan da ya kamace ta kenan.

Lawrence wanda ke wannan batu gabanin fafatawar Liverpool din da Madrid a wasan karshen na cin kofin zakarun Turai da zai gudana ranar 26 ga watan nan, ya ce ba wai yana kushe kokarin da ‘yan wasan ke yi bane, amma dai yana gargadi kan dole su yi taka tsantsan da Madrid wadda a cewarsa ba yawan kwallaye ta ke bukata ba, face zarra, inda ya ce Madrid din ka iya zura kwallo daya sannan ta koma kare kanta a wasan na ranar Asabar 26 ga watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.