Isa ga babban shafi
Wasanni

Tsaffin 'yan wasan Arsenal zasu yi bankwana da Wenger

Hukumar gudanarwar kungiyar Arsenal ta aikewa duk wani tsohon dan wasanta da ya buga mata wasanni 100 zuwa sama sakon gayyata, domin halartar bikin bankwana da mai horar da ita Arsene Wenger.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, tare da tsohon dan wasansa Thierry Henry.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, tare da tsohon dan wasansa Thierry Henry. AFP
Talla

Shahararren dan wasan Najeriya da ya ajiye takalmi Nwanko Kanu na daga cikin tsaffin ‘yan wasan kungiyar ta Arsenal da zasu halarci kallon wasan karshe a karkashin Arsene Wenger, wanda kungiyar zata yi a filinta na Emirates ranar Lahadi mai zuwa, inda zata fafata da Burnley.

Sauran tsaffin ‘yan wasan Arsenal da zasu halarci wannan wasa sun hada da Thierry Henry, Tony Adams, Bob Wilson, Frank Mac Lintock, Ian Wright da sauransu.

A cikin shekaru 22 da ya shafe yana horar da Arsenal, Wenger ya jagoranci kungiyar lashe kofunan gasar Premier 3 da kuma kofunan gasar FA 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.