Isa ga babban shafi
Wasanni

Saura kadan na koma horar da PSG a farkon kakar wasa - Wenger

Mai horar da Arsenal, Arsene Wenger ya ce kadan ya rage ya yi sallama da aikinsa a kungiyar, kafin sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu cikin watan Mayu.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger. Reuters/Paul Childs
Talla

Wenger ya bayyana haka yayin wata zantawa yayi da Jaridar Daily Mirror, inda y ace har yanzu a wajen fa akwai kwarin gwiwar Arsenal na da damar lashe kofin Premierer bana.

Dangane da batun ko akwai wata kungiya tayi masa tayin zuwa aikin horar da ita kuwa, Wenger ya ce kafin fara kakar wasa ta bana sai da kungiyar PSG ta tuntube shi, a kokarin ganin ya maye gurbin Umai Emery.

Tun kafin kammala kakar wasa shekarar bara ne dai mafi akasarin magoya bayan kungiyar ta Arsenal suka bukaci hukumar gudanarwar kungiyar ta sallami Wenger, bayanda a karon farko suka kasa samun tikitin zuwa gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai cikin shekaru 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.