Isa ga babban shafi
Wasanni

Gasar cin kofin duniya: Trump ya bukaci kuri'ar Najeriya

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci Najeriya da sauran kasashen nahiyar Afrika, su goyi bayan aniyar hadin gwiwar Amurkan, Canada da kuma Mexico na neman karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 2026.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Trump ya yi wannan kira ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar White House, bayan kammala tattaunawa da shugaban Najeriya Muhd Buhari, wanda ke ziyarar kwanaki 3 a Amurka.

Shugaban na Amurka ya ce zasu sa idanu domin lura da kasashen da zasu goyi bayan wannan aniya ta karbar bakuncin gasar cin kofin duniyar, za kuma su ga kyakkyawan sakamako.

A ranar 13 ga watan Yuni mai zuwa wakilan hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA zasu kada kuri’a don tantance wadanda za’a bai wa damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya tsakanin Amurka da kuma Morocco.

Sai dai fa akawai yiwuwar kalaman Trump ya sa Amurka ta fuskanci fushin FIFA, kasancewar dokokin hukumar, sun haramtawa gwamnati tsoma baki kai tsaye a harkokin da suka shafi sha’anin hukumomin kwallon kafa na kasashensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.