Isa ga babban shafi
wasanni

Rashin hadin kai ya cutar da Arsenal- Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya bayyana cewa, rashin hadin kai tsakanin magoya bayansu a wannan kakar, ya cutar da kungiyar.

Arsène Wenger na Arsenal
Arsène Wenger na Arsenal REUTERS/Phil Noble
Talla

Wasu daga cikin magoya bayan Arsenal na caccakar Wenger saboda fargabar rashin samun gurbi a jerin kungiyoyi hudu da ke saman teburin gasar fimiya karo na biyu a jere.

A jiya Lahadi ne dai Arsenal ta doke West Ham da ci 4-1, yayin da take mataki na shida akan teburin gasar.

Yanzu haka damar Arsenal ta zuwa gasar cin kofin zakarun Turai a badi ta ta’allaka ne akan lashe kofin Europa League.

A ranar jumm’ar da ta gabata ne, kocin dan asalin Faransa kuma mai shekaru 68 ya sanar da shirinsa na kawo karshen aikinsa a Arsenal nan da karshen kakar bana bayan shafe tsawon shekaru 22 yana horarwa a kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.