Isa ga babban shafi
wasanni

Roma ta kunyata Barcelona a gasar zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Roma ta nuna bajinta sosai bayan da ta doke Barcelona da kwallaye 3-0 a fafatawar da suka yi a matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, abin da ya ba ta damar tsallakawa matakin gaba na gasar, in da kuma Barcelona ta koma gida.

A karon farko tun shekarar 1984, Roma ta kai matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai
A karon farko tun shekarar 1984, Roma ta kai matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai REUTERS/Tony Gentile
Talla

An dai yi zaton cewa, mawuyaci ne Barcelona ba ta samu nasara akan Roma ba, lura da cewa, ita ke jan ragama da kwallaye 4-1 da ta zura a zagayen farko na fafatawarsu a Camp Nou.

Jim kadan da tashin wasan, ‘yan kallo da Kociyoyi suka fantsama cikin filin wasa na Stadio Olimpico don nuna murnar wannan nasara mai cike da mamaki da Roma ta samu akan Barcelona.

Wasu daga cikin magoya bayan Roma sai da suka zubar da hawaye saboda tsananin murna saboda ba su zaci hakan zai iya faruwa ba.

Yanzu haka Roma ta zama kungiya ta uku da ta kafa tarihi ta hanyar farke kwallaye sama da uku da aka zura ma ta a zagayen farko a gasar cin kofin zakarun Turai.

A karon farko tun shekarar 1984 dai, roma ta shiga matakin wasan dab da na karshe a gasar ta zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.