Isa ga babban shafi
Wasanni

Alkalan wasan Birtaniya ba zasu halarci gasar cin kofin Duniya ba

A karon farko cikin shekaru 80 wato tun daga 1938, babu wani alkalin wasa daga Birtaniya da zai halarci busa wasannin gasar cin kofin duniya da za’a yi a Rasha.

Alkalin wasa dan kasar Birtaniya Mark Clattenburg.
Alkalin wasa dan kasar Birtaniya Mark Clattenburg. AP
Talla

Wannan tarihi mai daukar hankali a duniyar wasanni ya tabbata ne bayan da FIFA ta wallafa sunayen alkalan wasa 36 da mataimakansu 63 da ta zaba domin busa a wasannin da za’a yi, ba tare da bayyanar sunan ko da Alkalin wasa day aba daga Ingila, Scotland, Wales da kuma Northern Ireland.

Zalika babu dan Birtaniya a cikin mataimakan alkalan wasa 63 da zasu yi aiki yayin wasannin na gasar cin kofin duniya.

A shekarar 2016 dai, Mark Clattenburg shi ne alkalan wasa daya tilo daga kasar Birtaniya da sunansa ke cikin jerin wanda hukumar FIFA ta tattara, kafin daga bisani ya janye.

A halin yanzu dai alkalan wasa da kuma mataimakansu da FIFA ta zabo daga nahiyar turai sun fito ne daga kasashen Jamus, Faransa, Rasha, Holland, Poland, Spain, da Italiya, sai kuma Turkiya, Slovenia, da kuma Serbia.

Wannan na zuwa yayin da dangantaka ta yi tsami tsakanin Rasha da Birtaniya wadda kawayenta suka mara mata baya, wajen korar jami’an dilflomasiyar Rasha akalla 150 daga kasashensu, saboda zargin Rasha na da hannu wajen sanyawa tsohon jami’in leken asirin Birtaniya Sergai Skrippal da ‘yarsa Yulia Guba gidansa da ke Salisbury a Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.