"Neymar zai iya shafe watanni 5 yana jinya
Wani kwararren likita a kudancin Amurka Carlinhos Vidente, ya yi hasashen Neymar ba zai samu damar bugawa kasarsa Brazil wasannin da za ta yi na cin kofin duniya a Rasha ba.
Wallafawa ranar:
Vidente, ya bayyana haka ne, yayin da ya ke gargadin cewa Neymar zai shafe tsawon watanni 5 zuwa 7 yana jinyar raunin da ya samu a kafa, muddin ana bukatar ya warke sarai.
Neymar ya samu raunin ne a wasan da suka lallasa kungiyar Marseille da kwallaye 3-0 a watan Fabarairu da ya gabata, kuma da farko an yi zaton gurdewa ya yi a kafa.
Daga bisani ne likitoci suka gano cewa ya samu tsagewar kashin kafarsa da ke hade da ‘yan yatsu 'Metatarsals' a turance.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu