Isa ga babban shafi
Wasanni

Roma ta tsallake rijiya da baya

Kungiyar Roma ta samu kai wa ga matakin gaf da kusa da na karshe, bayan samun nasara akan Shaktar Donetsk da 1-0.

'Yan wasan kungiyar AS Roma a filin wasa na Stadio Olimpico, da ke birnin Rome, a Italiya,  bayan samun nasara akan kungiyar Shaktar Donetsk.
'Yan wasan kungiyar AS Roma a filin wasa na Stadio Olimpico, da ke birnin Rome, a Italiya, bayan samun nasara akan kungiyar Shaktar Donetsk. REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

Dan wasan gaba na Roma Edin Dzeko ne ya ci wa kungiyar tasa kwallon a mintuna na 52.

A zagayen farko na wasan da suka buga a Ukraine, Roma ta yi rashin nasara a hannun Shaktar Donetsk da kwallaye 2-1.

Karo na farko kenan da AS Roma ta samu kai wa ga zagayen gaf da kusa da karshe a gasar ta zakarun nahiyar turai cikin shekaru 10.

Zalika rabon da wasu kungiyoyin kwallon kafa da suka fito daga kasar Italiya su kai matakin na gaf da kusa da karshe, kamar wannan karon a lokaci guda, tun bayan kakar wasa ta 2006/2007, a lokacin da kungiyar ta Roma, da AC Milan suka samu nasarar kai wa zagayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.