Isa ga babban shafi
wasanni

Za a fara duba lafiyar Kane bayan raunin da ya samu

A wannan Litinin ake saran daukan hoton sahun dan wasan Ingila Harry Kane don nazarin raunin da ya samu a yayin faftawar da kungiyarsa ta Tottenham ta lallasa Bournemouth da ci 4-1 a jiya Lahadi a gasar firimiya.

Harry Kane ya ci wa Tottenham kwallaye 35 a kakar bana
Harry Kane ya ci wa Tottenham kwallaye 35 a kakar bana Paul Childs/Reuters
Talla

Raunin ya tilasta sauya Kane mai shekaru 24 bayan minti 30 da fara wasan, in da ya gaggauta ficewa daga fili.

Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino ya ce, yana fatan raunin ba zai kasance babba ba, amma za su ci gaba da zura idanu.

Ko a kakar da ta gabata, sai da Kane ya yi fama raunin da ya tilasta masa rasa wasanni 10

Harry Kane ya ci wa Tottenham kwallaye 35 a kakar bana, kuma a ranar Asabar mai zuwa ne kungiyarsa za ta kara da Swansea a gasar FA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.