Isa ga babban shafi
wasanni

Toni Kroos ya samu rauni a gwiwa

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tabbatar da raunin da dan wasan tsakiyarta Toni Kroos ya samu a gwiwarshi ta hagu. Akwai dai rade-radin da ke cewa dan wasan ka iya daukar lokaci kafin murmurewa amma Real din ta ki bayyana gaskiyar batun.

Tawagar 'yan kwallon Real Madrid.
Tawagar 'yan kwallon Real Madrid. © REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Bayan gwaje-gwaje a cewar Real Madrid an gano dan wasan ya samu mummunan rauni yayin karawarsu da PSG lokacin da suka yi wata taho mu gama da Kylian Mbappe a wasan da suka yi nasara da ci 3 da 1 ranar larabar da ta gabata.

Kroos dan kasar jamus mai shekaru 28 wanda ya taka leda a tsawon mintuna 90 na wasan daya gudana tsakanin su da PSG din ranar larabar makon nan Madrid na fatan ya kammala murmurewa gabanin wasan da za su bi PSG gida a ranar 6 ga watan Maris.

Tuni dai wasu suka fara hasashen cewa PSG din ka iya rama abin da Madrid din ta yi mata a wasan na ranar Laraba, ko da ya ke dai Kocin Madrid Zinadine Zidane ya ce za su yi gagarumin shiri don tunkarar wasan na ranar 6 ga watan Maris a Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.