Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya kafa tarihi a Gasar Zakarun Turai

Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa na farko a tarihin Gasar Zakarun Turai, da ya ci wa kungiyar da yake bugawa kwallaye 100, idan aka tattara ilahirin wasannin gasar ta UEFA da ya buga mata.

Cristiano Ronaldo; lokacin da yake murnar zura kwallo ta biyu, a ragar PSG, a wasan Gasar Zakarun nahiyar Turai.
Cristiano Ronaldo; lokacin da yake murnar zura kwallo ta biyu, a ragar PSG, a wasan Gasar Zakarun nahiyar Turai. REUTERS/Paul Hanna
Talla

Ronaldo ya kafa tarihin ne bayan zura kwallaye biyu a ragar kungiyar PSG da ta yi tattaki daga Faransa zuwa Spain, a zagayen farko na matakin kungiyoyi 16 a gasar zakarun turan.

A wasan na jiya dai Real Madrid ta lallasa PSG da kwallaye 3-1, kuma dan wasan baya na Madrid Marcelo ne ya jefa kwallo ta ukun, yayin da ita kuma PSG dan wasanta, Rabiot ya ci mata kwallo tilo.

A halin yanzu Cristiano Ronaldo ya fi kowane dan wasa yawan kwallaye da ya ci a tsawon lokacin da ya shafe yana buga gasar zakarun turai, domin kuwa yana da kwallaye 115.

Lionel Messi shi ne ke biyewa Ronaldo da kwallaye 97, yayin da tsohon dan wasan Real Madrid Raul Gonzàles yake matakin dan wasa na uku da kwallaye 71.

Sauran ‘yan wasan da suke kan gaba wajen yawan kwallayen da suka ci a gasar zakarun turai kadai, sun hada da Ruud van Nistelrooy, tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid, da ya ci kwallaye 56, sai na biyar dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema, mai kwallaye 53.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.