Isa ga babban shafi
wasanni

Kloop ya yi bakin cikin canjaras da Tottenham

Kocin Liverpool Jurgen Kloop bai ji dadin yadda suka yi canjaras da Tottenham 2-2 ba a gasar Premier ta Ingila bayan alkalin wasa ya bai wa Tottenham bugun fanariti a minti na 95, abin da ya bai wa Hary Kane damar zura kwallo ta 2.

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp Reuters/Craig Brough
Talla

Kane ya barar da bugun fanaritin da aka fara ba shi, amma ya yi nasarar zura kwallo a dama ta biyu, in da kuma a jumulce ya zura kwallaye 100 a gasar Premier.

Kwallon da Kane ya zura ta matukar bakanta ran magoya bayan Liverpool da suka yi shirin bikin murna, bayan sun yi amanna cewa, kwallon da Mohammed Salah ya zura a minti na 91 za ta ba su nasarar lashe wasan amma lamari ya sauya a cikin kankanin lokaci.

A cewar Jurgen Kloop, da zai bayyana hakikanin yadda ransa ya baci, to lallai da hukukomin kwallon kafar Ingila sun dauki mataki mai tsauri a kansa tare da cin sa tarar da ba a taba cin wani ba a duniyar tamaula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.