Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester United ta saye Alexis Sanchez

Kungiyar Manchester United ta saye Alexis Sanchez na Arsenal kan yarjejeniyar da ya kunshi musanya dan wasan da Henrikh Mkhitaryan.

Alexis Sanchez ya kulla yarjejeniyar komawa Manchester United
Alexis Sanchez ya kulla yarjejeniyar komawa Manchester United Reuters / Carl Recine
Talla

Sanchez dan kasar Chile mai shekaru 29 ya cim-ma yarjejeniya kwantiragi shekaru 4 da rabi da United akan fan miliyan 14 bayan haraji.

Man City da ta so daukan dan wasan tun a bara, a makon da ya gabata ta ce ta fasa cinikin saboda Sanchez zai kasance mafi tsada a kungiyar.

Mkhitaryan mai shekaru 29 kuma zai koma gurbin Sanchez bayan zura kwallaye 13 a wasanin 63 da ya bugawa United.

A watan Yuli 2016 Mkhitaryan dan asalin Armenia ya koma Old Trafford daga Borussia Dortmund kan fan milyan 26.3

Arsenal za ta haska Mkhitaryan a wasan Frimniyar da za ta fafata da Swansea ranar 30 ga watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.