Isa ga babban shafi
Wasanni

Sir Alex Ferguson ya taya Wenger murnar kafa sabon tarihi

Tsohon mai horar da kungiyar Manchester United Sir Alex Ferguson, ya taya kocin Arsenal Arsene Wenger, murnar kafa sabon tarihin zama mai horarwa daya zarta takwarorinsa yawan jagorantar wasanni gasar Premier.

Tsohon mai horar da kungiyar Manchester United Sir Alex Ferguson tare da mai horar da Arsenal Arsene Wenger.
Tsohon mai horar da kungiyar Manchester United Sir Alex Ferguson tare da mai horar da Arsenal Arsene Wenger. Reuters
Talla

Ferguson ya ce zai yi wahala a nan kusa a samu wani mai horarwa a gasar ta Premier da zai shafe tarihin da Wenger ya kafa na jagorantar wasanni 811 a tsawon shekaru 20, da ya shafe yana horar da Arsenal bayan wasansu da West Brom da aka fafata a ranar Lahadi da ta gabata.

Kafin wannan lokacin, Tsohon mai horar da kungiyar Manchester United Sir Alex Ferguson, ya fi kowane mai horar yawan jagorantar wasanni a gasar Premier, inda yake da wasanni 810.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.