Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester City ta bai wa United tazarar maki 15

Kungiyar Manchester City, ta bai wa takwararta ta Manchester United da ke biye da ita a matsayi na biyu bisa teburin gasar Premier tazarar maki 15, bayan wasan da ta samu nasara kan Newscastle da kwallo daya mai ban haushi. 1-0.

'Yan wasan kungiyar Manchester City bayan lallasa Newcastle United da 1-0. Disamba 27, 2017.
'Yan wasan kungiyar Manchester City bayan lallasa Newcastle United da 1-0. Disamba 27, 2017. REUTERS/Scott Heppell
Talla

Raheem Sterling ne ya jefawa Cityn kwallo a ragar Newcastle, yayin wasan da Mai horar da City Pep Guardiola ya bayyana shi a matsayin mai wahala, idan aka yi la’akari da yadda ‘yan wasan Newcastle suka rika nuna dagiya wajen tsaron gida fiye da fitowa neman zura kwallo.

Yayin wasan, Manchester City ta zarta Newscastle wajen rike kwallo da shafawa, inda Cityn ta ke da maki 78 Newcastle da ragowar, yayinda a bangaren kai hare-haren zura kwallaye masu hatsari, City ke da 21 Newscastle kuma ta kai kwararan hare-hare sau 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.