Isa ga babban shafi
Wasanni

Sahararren mai wasa da bijimin Sa ya rasa ransa

Shahararren mai wasa da bijimin sa dan kasar Spain, Ivan Fandino, ya rasa ransa, sakamakon yamutsa shi kamar kayan wanki, da wani jibgegen Sa, da yake wasa da shi yayi.

Ivan Fandino, yayinda bijimin Sa da yake wasa da shi ya fara sukarsa da kaho.
Ivan Fandino, yayinda bijimin Sa da yake wasa da shi ya fara sukarsa da kaho. youtube
Talla

Fandino mai shekaru 36, ya gamu da bacin ranar ce, a lokacin da yake tsala gudu cikin da’irar filin da yake tsaka da nuna bajintarsa ta wasa da San, a kudu maso yammacin kasar Faransa, a bikin wasan da aka saba duk shekara, inda ya harde ya fadi, shi kuwa bijimin Sa ya cigaba da tumurmusa shi, har kahonsa ya soke masa huhu.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa sau biyu Fandino yana samun bugawar zuciya kafin a karasa da shi asibiti, inda rai yayi halinsa.

A watan Yulin shekara ta 2016 ma, wani sanannen mai wasan gangancin da bijimin Sa, Victor Barrio, ya rasa ransa, a lokacin da yake tsaka da wasa, bayanda San ya soke masa kirji da kaho.

A kalla mutane miliyan shidda ne a kasar Spain ke halartar wuraren da ake irin wannan wasa, wanda masu rajin kare hakkin dabbobi ke matukar adawa da shi, kuma mutuwar ‘yan wasan da aka samu a baya bayannan ya sanya masu fafutukar kara kaimi wajen ganin hukumomi sun haramta wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.