Isa ga babban shafi
Wasanni

Tarzoma ta barke lokacin karawar Lyon da Bastia

Tarzoma ta barke a daidai lokacin da ya kamata a fara buga wasan Ligue 1 ta Faransa tsatsakanin Lyon da kuma Bastia, lamarin da ya sa aka soke buga wasan sai zuwa nan gaba.

Artabu a lokacin karawar Lyon da Bastia
Artabu a lokacin karawar Lyon da Bastia AFP
Talla

A wannan karo magoya bayan Bastia ne suka tayar da tarzomar daidai lokacin da ‘yan wasa suka fara fitowa fili dominkarawa, lamarin da ya tilasta wa jami’an tsaro yin amfani da hayaki mai sa kwalla domin tarwatsa su daga filin wasan.

Ko a ranar alhamis ta makon jiya an samu irin wannan rikici tsakanin magoya bayan Lyon da kuma Besiktas ta kasar Turkiyya, lamarin da ya sa aka dakatar da wasan da akalla mintuna 50, to sai dai a wancan karo magoya bayan Lyon ne suka tayar da rikicin ta hanyar jifa akan abokannin hamayyar ‘yan Turkiyya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.