Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

AC Milan ta yi kunnen doki da PSV, Lyon ta sha kashi a hanun Real Sociedad da ci 2-0

A wasannin da aka fara bugawa na shiga rukunin buga gasar Zakarun Nahiyar Turai, wato Champions League. Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta tashi da ci 1-1 tskaninta da kungiyar PSV Eindhoven a Netherland.

Mai tsaron gidan AC Milan, Philippe Mexes
Mai tsaron gidan AC Milan, Philippe Mexes AFP/Olivier Morin
Talla

A Faransa kuwa Lyon ta sha kashi a hanun Real Sociedad da ci 2-0 yayin da Zenith St. Petersburg ta lallasa Pacos de Ferreira da ci 4-1.

A yau laraba kuma Dinamo Zagreb ta kasar Croatia za ta karbi bakuncin Austria Vienna a Austria kana Arsenal ta kaiwa Fenerbache ziyara a Turkiya.

Ita kuwa Schalke 04 ta kasar Jamus za ta fafata ne da PAOK Girka.

A fagen gasar Premier kuwa a yau za ta karbi bakuncin Aston Villa wacce ta lallasa Arsenal da ci 3-1 a wasansu na farko.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.