Isa ga babban shafi
Wasanni

Maki hudu ne tsakanin Chelsea da Tottenham

Bayan share tsawon watanni tana jagorantar teburin gasar Premier a Engila, a jiya lahadi kungiyar Chelsea ta sha kashi a hannun Manchester United ci 2 da nema, lamarin da ya haddasa raguwar tazarar makin da ke tsakanin Chelsea da Tottenham zuwa maki 4 kacal.

Karawar Man-U da Chelsea a ranar 16-04-2017
Karawar Man-U da Chelsea a ranar 16-04-2017
Talla

Wannan dai na nufin cewa dole ne Chelsea ta matsa kaimi domin ci gaba da kasancewa jagora a gasar ta Premier, yayin da ya rage ma ta wasanni 5 kafin kawo karshen kakar wasanni ta bana.

Rashaford da kuma Herrera ne suka zura wa Man-U kwallaye a ragar Chelsea a mintuna na 7 da kuma na 49 bayan fara wasan wanda aka yi a gidan Man-U.

Manajan Chelsea da kansa Antonio Conte, ya ce lalle akwai babban kalubale a gabansu kafin su iya daukar kofin Premier na bana, inda yake cewa idan har ma suna da sa’ar daukar wannan kofi, to sa’ar ba za ta wuce kashi 50 cikin dari ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.