Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Bayern Munich ta caccasa Arsenal

Bayern Munich ta lallasa Arsenal 5-1 a fafatawar da suka yi a Allianz Arena a gasar zakarun Turai zagaye na biyu. Real Madrid ma ta doke Napoli ci 3-1 a Santiago Bernabeu.

Arjen Robben ya fara ci wa Bayern Munich kwallo a ragar Arsenal
Arjen Robben ya fara ci wa Bayern Munich kwallo a ragar Arsenal REUTERS
Talla

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya karbi laifin kashin da ‘yan wasan shi suka sha a hannun Bayern Munich.

Sau uku Bayern na fitar da Arsenal a 2005 da 2013 da 2014 daidai wannan zagaye na biyu a gasar zakarun Turai.

Kuma yanzu yana da wahala ga Arsenal ta iya rama kwallayen a haduwar da za su sake yi a Emirate a ranar 7 ga watan Maris.

Wenger ya shafe shekaru 20 yana horar da Arsenal amma sakamakon wasansu da Bayern na yin barazana ga makomar shi a kungiyar.

Yanzu Bayern Munich za ta yi waje da Arsenal a karo na hudu a gasar zakarun Turai.

Ana minti 11 da fara wasa Arjen Robben ya fara bude ragar Arsenal inda ya yanke Gola amma Alexis Sanchez ya farke kwallon kafin aje hutun rabin lokaci bayan ya barar da fanariti.

Cikin mitina uku Bayern Munich ta jefa kwallaye biyu a ragar Arsenal bayan dawowa hutun rabin lokaci.

Kwallaye biyu Thiago Alcantara ya jefa a raga yauyin da Robert Lewandowski da Thomas Mueller da suka ci wa Bayern sauran kwallayen.

Madrid ta doke Napoli

Karim Benzema da Toni Kroos da Casemiro ne suka ci wa Real Madrid kwallayenta a ragar Napoli.

Napoli ce ta fara cin Madrid ana minti 10 da soma wasa, inda daga wajen 18 Lorenzo ya auna Golan Madrid bayan ya fito.

Madrid na da kwarin guiwar tsallakewa zuwa zagayen kwata fainal a karawar da za ta sake yi da Napoli a Italiya, domin kare kofin da ta lashe a bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.