Aguero ba zai karawa Argentina ba saboda rauni
Raunin da dan wasan Manchester City Sergio Aguero ya samu a karawarsu da West Ham ranar lahadi karshan mako, zai hana dan wasan haskawa Argentina a wasannin neman gurbi a gasar cin kofin Duniya na shekarar 2018 da ake cigaba da fafatawa.
Wallafawa ranar:
Hukumar kwallon kafar Argentina dake sanar da halin da dan wasan mai shekaru 28 ke ciki, ta ce babu wani tsayayyen lokacin da ake gani dan wasan zai warware.
A ranar jumaa Argentina zata fafata da Uruguay, kana ranar 7 ga watan Satumba ta fuskanci Venezuela.
Lionel Messi daya janye matakin daya dauka na yin ritaya, zai haska a wasan don tuni ya shiga atisaye da tawagar Argentina.
Argentina dai ta cinye 3 daga cikin wasannita 6 da zata fafata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu