Isa ga babban shafi
Olympics

Tarihin wasannin Olympics

Gasar Olympics ta samo asali ne kimanin shekaru 2,700 a birnin Olympia da ke kudu maso yammacin kasar Girka. Tarihi ya nuna cewa an kirkiro gasar ce domin karrama abin bautar mutanen yankin a waccan lokaci.

Tambarin gasar Olympic
Tambarin gasar Olympic REUTERS/David Gray
Talla

A kwana a tashi wasannin motsa jikin da aka fara a shekara ta 776 ita ce ta kai ga haifar da gasar Olympic din da muka saba gani a yanzu, da aka fara a 1896, kuma ana gudanar da wasannin ne duk bayan shekaru hudu.

Pierre de Coubertin, shi ne ya kafa hukumar kula da gasar Olympics IOC, wadda ta kawo sauye-sauye na zamani da yanzu ake gani a gasar, musamman daga karni na 20 zuwa na 21.

Wadannan sauye-sauye sun hada da kirkirar gudanar da gasar a lokacin zubar kankara, kirkiro gasar masu fama da nakasa (masu bukata ta musamman) da aka fi sani da Paralympics, sai kuma kirkirar sashin gasar na kananan yara zalla.

Sai dai a shekarun baya wannan gasa ta Olympics ta gamu da matsalolin da suka sa ba a gudanar da wasannin ba a wasu shekaru, misali a shekarun 1916, 1940 da kuma 1944 yake-yake sun sanya a dakatar da wasannin motsa jikin na Olympics.

Wani kalubalen da gasar Olympics din ta fuskanta shi ne yadda a shekarun 1980 da kuma 1984 rashin jituwa tsakanin wasu daga cikin manyan kasashen duniya ya sa ba ta yi armashi ba saboda karancin wadanda suka halarci wasannin.

Hukumar kula da Olympics IOM ke da alhakin zabar kasar da za ta karbi bakuncin gasar, tare da tsara yadda gasar za ta gudana.

Sama da ‘yan wasa 13,000 uku ne suke fafatawa a ire-iren wasanni 33 cikin zagaye 400. Yayin da ‘yan wasan da suka samu nasarar kame matakan na daya da na biyu da kuma uku suke samun lambar yabon Zinare, Azurfa, da kuma Tagulla.

Yanzu haka gasar Olympics ta yi shaharar da kusan kowace kasa na tura wakilanta don samo lambar yabo, kasancewar a yanzu kasashe 206 ne za su barje gumi a gasar Olympics ta bana a Birnin Rio na kasar Brazil.

Biyo bayan shaharar wannan gasa, zarge-zargen kan aikata laifuka don samu nasara ayayin gasar sun sha tasowa kamar cin hanci, shan kwayoyin samun Karin kuzari da kuma matsalar yunkurin kai harin ta’addanci yayin da gasar ke gudana.

Ko a wannan shekarar sai da ‘yan sandan kasar Brazil suka kame wasu ‘yan kasar goma bisa zarginsu da kitsa kai hari lokacin da ake tsaka da gasar a birnin Rio.

A bangare guda kuma duk dai a wannan shekara sama da ‘yan wasan kasar Rasha 100 aka haramtawa shiga gasar ta Olympics saboda samunsu da laifin shan kwayoyin Karin kuzari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.