Isa ga babban shafi
Wasanni

IOC za ta gana kan makomar Rasha a Olympics

Yau ne mambobin kwamitin kula da wasannin Olympics na duniya za su yi ganawar gaggawa, inda za su cimma matsaya kan batun shigar kasar Rasha cikin wasannin Olympics domin a fafata da ita a birnin Rio ko akasin haka.

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Thomas Bach da mataimakinsa John Coates da shugaban kwamitin wasannin Olympics na Japan Tsunekazu Takeda a Tokyo
Shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Thomas Bach da mataimakinsa John Coates da shugaban kwamitin wasannin Olympics na Japan Tsunekazu Takeda a Tokyo Reuters/路透社
Talla

Wannan na zuwa ne bayan wani bincike ya nuna yadda gwamnatin kasar ta taimaka wa ‘yan wasanta wajen kwan-kwadan kwayoyin kara kuzari a wasannin Olympics da aka gudanar a shekara ta 2014 a Sochi na Rasha.

Hukumar da ke yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta duniya ta bukaci a haramta wa Rasha shiga wasannin Olympics da za a fara a watan gobe a Rio de Janeiro na Brazil saboda kaurin sunan da ‘yan wasanta suka yi wajen shan kwayoyin.
 

A bangare guda hukumar da ke yaki da shan kwayoyin ta bukaci hukumar kwallon kafa ta duniya da ta binciki ministan wasannin Rasha, Vitaly Mutko wanda mamba a kwamitin gudanarwa na FIFA bayan rahoton ya ce, a  ma’aikatarsa nada masaniya kan shan kwayoyi tsakanin ‘yan wasa amma ba ta dauki wani mataki ba.
 

Kasar Rasha dai na shirye-shirye daukan bakwancin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.