Isa ga babban shafi
Zurich

Indonesia da Kuwait ba zasu Jefa Kuri'ar Zaben Sabon Shugaban FIFA ba

Hukumar kula da harkokin kwallon kafa ta duniya ta ce kasar Indonesia da Kuwait wadanda aka kora daga harkan kwallon kafa na duniya , za'a  hana su jefa kuri'a a zaben shugabancin FIFA.

Hoton 'Yan takaran shugabancin Hukumar FIFA
Hoton 'Yan takaran shugabancin Hukumar FIFA AFP PHOTO
Talla

Wannan bukata na nuna zai yi wuya kasashen biyu su jefa kuria a zaben Juma''a inda za’a zabi sabon shugaban Hukumar, al’amari da zai shafi dan takaran dake kan gaba Sheikh Salman bin Ebrahim al Khalifa.

Hukumar wasannin kwallon kafa ta Asia, da ta kunshi Indonesia da Kuwait, ta amince masa da shiga takaran.
A halin da ake ciki kuma an rage wa'adin hukuncin da aka zartas kan tsohon shugaban Hukumar FIFA Sepp Blatter da kuma Michel Platini.

Komitin Daukaka kara na hukumar FIFA ta zartas da rangwamen, na dakatar da mutanen biyu daga tsawon shekaru takwas zuwa shida.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.